Hanyoyin Samun Ciki da Wuri: Jagora Ga Matan da Ke Son Haihuwa Da Wuri
Shin kina son samun ciki da wuri? Ko kin dade kina kokarin samun ciki amma har yanzu ba labari? Akwai wasu hanyoyin samun ciki da wuri da zaki iya bi domin samun ciki cikin kankanin lokaci. A cikin wannan post, za mu tattauna hanyoyi masu amfani da za su taimaka miki wajen inganta lafiyar haihuwa da kuma saurin samun juna biyu.
1. Fahimtar Lokacin Da Kike Daukar Ciki
Lokacin ovulation (lokacin da kwai ke fita daga mahaifa) shine mafi dacewa da samun ciki. Ga matan da ke da haila mai tsari (misali, kowace rana 28), ovulation na faruwa ne a rana ta 14 daga farkon haila. Idan haila tana da tsawon kwanaki 30, ovulation zai kasance kusan rana ta 16.
Yadda Ake Sanin Ovulation:
- Yin amfani da ovulation test kit.
- Kula da jikin ki, domin wasu matan suna jin dan ciwo a ciki ko karin farin ruwa daga farji.
- Duba canje-canjen yanayin mucus na farji (yana zama kamar rawan kwai a lokacin ovulation).
Don samun ciki da wuri, yana da kyau ki yi jima’i kwanaki 3–5 kafin ovulation da kuma a ranar da ovulation ke faruwa.
2. Yawaita Yin Jima’i a Lokacin Da Ya Dace
Yin jima’i sau 3-4 a mako (ko kowane kwana biyu) yana kara yiwuwar daukar ciki. Yana da kyau a yi jima’i a ranakun da ovulation ke kusa domin samun sakamako mai kyau.
Shawarwari:
- Kada ki yi amfani da man shafe-shafe a yayin jima’i (lubricants) wadanda ba na musamman ba, saboda suna iya kashe maniyyi.
- Ki huta bayan jima’i na wasu mintuna 10-15 kafin ki tashi.
3. Inganta Lafiyarki Da Abinci Mai Gina Jiki
Abinci yana taka muhimmiyar rawa wajen samun ciki cikin sauki. Ki tabbata kin cika jiki da abubuwa masu gina jiki.
Abinci Mai Amfani:
- Vitamin C da E: Yana inganta lafiyar maniyyin maza da kwai na mata.
- Folic Acid: Yana taimakawa wajen lafiyar mahaifa da rage matsalolin nakuda.
- Zinc da Iron: Yana taimakawa wajen inganta kwayoyin halittar haihuwa.
- Kayan lambu da fruit: Yana kara kuzari da lafiyar kwakwalwa.
- Madara da hatsi: Suna taimakawa wajen daidaita hormones.
Abinci kamar shinkafa, kifi, doya, kankana, avocado, da kifi mai kitse (salmon, sardine) suna kara yiwuwar samun ciki.
4. Gujewa Abubuwan da Zasu Hana Samun Ciki
Akwai wasu abubuwa da ke rage yiwuwar samun ciki da wuri, kamar:
- Shan sigari da giya.
- Yawan shan caffeine fiye da kofi 2 a rana.
- Matsanancin kiba ko rama sosai.
- Yawan damuwa da gajiya.
Yin motsa jiki mai sauki kamar tafiya, yoga, ko aerobic yana taimakawa wajen daidaita hormones na jiki.
5. Magunguna Da Karin Wasu Shawarwari
Idan bayan watanni 6 zuwa shekara guda kina kokarin samun ciki amma ba labari, yana da kyau ki ga likita. Za su iya duba lafiyar ki da ta mijin ki don gano matsalar.
Akwai wasu magunguna kamar Clomid, Letrozole, da Gonadotropins da likitoci ke bada wa matan da ke da matsalar daukar ciki.
Kammalawa
Samun ciki da wuri yana bukatar fahimta, hakuri, da kula da lafiyar jiki. Ki tabbata kina jima’i a lokutan da suka dace, kina cin abinci mai kyau, da gujewa abubuwan da ke rage yiwuwar samun ciki. Idan kina da wata matsala, likita zai iya taimakawa wajen nemo mafita.
Idan kin bi wadannan hanyoyin samun ciki da wuri da muka ambata a sama, insha Allah za ki samu juna biyu cikin lokaci kadan!