Yadda Ake Hada Maganin Sanyi

Yadda Ake Hada Maganin Sanyi

Yadda Ake Hada Maganin Sanyi: Cikakken Bayani da Matakai

Yadda ake hada maganin sanyi
Cike da bincike irin na masu neman ilimi, mun kawo yadda ake hada maganin sanyi na gargajiya ko na Bature, domin dai masu neman hanyoyin da zasu kare kansu ko rabuwa da wannan ciwo na sanyi.

Cutar sanyi wacce aka fi sani a turance da infection wata matsala ce data ke shafar lafiyar mata dama maza gaba ɗaya, musamman idan ya kasance ba'a dauki matakan kariya ba. Ana samun sanyi ta hanyoyi daban-daban, ciki har da rashin tsafta, rashin kula da jiki, ko kamuwa da kwayoyin cutar ta infection. A wannan rubutu, zamu yi bayani dalla-dalla kan yadda ake hada maganin sanyi, Kuma tareda yin amfani da kayan gargajiya da na zamani domin magance wannan cuta ta sanyi.

Menene Sanyi?

Sanyi wani nau'in rashin lafiya ne da ake danganta shi da kamuwa da cututtuka a sassan jiki kamar irin su mafitsara, mahaifa, farji, ko al'aurar maza. Wannan matsala ta sanyi (infection) na iya haifar da ciwon ciki, jin zafi lokacin fitsari, ko kaikayi. Ayi sani cewa mafi yawan lokuta, sanyi na faruwa ne sakamakon kwayoyin cuta da suka shiga jiki ta hanyoyi kamar:

(1). Rashin amfani da bayan gida mai tsafta.

(2). Yin saduwa da wanda ke dauke da cutar.

(3). Amfani da sabulu (soap) wanda bai dace ba wajen tsaftar al'aura.

(4). Rashin wanke hannaye yadda ya kamata bayan amfani da bayan gida.

Ire-Iren Sanyi

Sanyi na Mafitsara wanda aka fi sani da (UTI): Wannan irin sanyi na faruwa ne idan kwayoyin cuta suka shiga mafitsara, suna haifar da zafi yayin yin fitsari.

Sanyi na Farji: Wannan shine wanda ke haifar da ƙaikayin gaba ko fitar ruwa mai wari daga farjin mace.

Sanyi na Mahaifa: Wannan nau'in sanyi yafi matukar tsanani, domin yana iya haifar da ciwon ciki mai zafi ko matsala wajen haihuwa idan ba'a nemi magani ba.

Yadda Ake Hada Maganin Sanyi: Da Kayan Gargajiya

Ga wasu jerin kayan gargajiya masu tasiri da yadda ake hada maganin sanyi da su:

1. Ganyen Zogale

Ganyen zogale yana da sinadaran antibacterial dake taimakawa wajen kashe kwayoyin cutar sanyi.

Yadda ake haɗawa:

A sami ganyen zogale, ki wanke shi da kyau.

Ki tafasa shi a cikin ruwan zafi na tsawon mintuna 15.

Sannan sai ki tace ruwan, ki sha da ɗuminsa kullum sau biyu a rana.


2. Citta da Tafarnuwa

Citta da tafarnuwa suma suna dauke da sinadarai dake magance kwayoyin cutar ta sanyi har ma da kumburi.

Yadda ake haɗawa:

Bayan kin samu tafarnuwa da citta sai ki markaɗasu a tare.

Ki tafasa su a cikin ruwa na tsawon kamar mintuna 10.

Ki tace ruwan, ki sha kullum da dumi kullum sau biyu a rana.


3. Kanumfari

Kanumfari na taimakawa matuƙa gaya wajen rage kaikayi da kuma fitar ruwa daga farjin mace sakamakon ciwon sanyi.

Yadda ake hada shi:

Ki samu kanumfari, ki niƙa shi ya zama gari.

Sannan ki tafasa cokali daya na garin kanumfari a cikin ruwan zafi na tsawon mintuna 10.

Ki tace ruwan, ki sha shima sau biyu a rana.


4. Ganyen Magarya

Ganyen magarya yana taimakawa kwarai da gaske wajen tsaftace jiki daga kwayoyin cuta.

Yadda ake haɗashi:

Ki samu ganyen magarya mai kyau, ki wanke shi yadda ya kamata.

Ki tafasa ganyen a cikin ruwa na tsawon mintuna 15.

Ki tace ruwan, ki sha da ɗuminsa sau biyu ko uku a kowace rana.


5. Zuma da Lemon Tsami

Zuma musamman farar saƙa tana dauke da sinadaran antibacterial wato masu kashe bacteria babu sausauci, yayinda shi kuma lemon tsami ke taimakawa wajen gyaran adadin Hydrogen dake jiki.

Yadda ake hada su:

Ki matse lemon tsami yanda ya sawwaƙa a cikin kofi.

A zuba zuma cokali biyu.

Sai ki hada da ruwan dumi, ki sha sau uku wato safiya rana da maraice.


Yadda Ake Maganin Sanyi da Kayan Zamani

Ga waɗanda basa son yin amfani da kayan gargajiya domin keta haddin cutar sanyi, zasu iya amfani da magungunan asibiti kamar:

Antibiotics: Magunguna irinsu Amoxicillin ko Ciprofloxacin suna taimakawa wajen kashe kwayoyin cutar infection ta sanyi. Amma duk da haka, yana da kyau ayi amfani dasu bisa shawarar likita ko kuma masani.

Antifungal Creams: Idan sanyin dake damunki na farji ne, kina iya amfani da maganin shafawa kamar Clotrimazole domin rage kaikayi da fitar ruwa.

Pain Relievers: Idan kina yawan jin ƙaikayi ko raɗadi, likita na iya baki magungunan rage zafi kamar Ibuprofen.

Duka abinda nayi bayani a sama idan aka je Chemist ko asibiti za'a iya samunsu.


Hanyoyin kariyar kamuwa da Cancer daga Sanyi

Domin kariya daga kamuwa da sanyi ko hana dawowarsa, ya kamata abi waɗannan matakan:

Tsafta: Ki tabbata kina wanke hannunki kafin shiga da bayan amfani da bayan gida.

Rage Caffeine: Yana da kyau ki rage shan abubuwan sha masu dauke da caffeine, kamar Pop-cola, Coca-Cola da Passion domin suna iya kawo matsala wajen fitsari.

Amfani da Condoms: Idan ke matar aure ce domin kariya lokacin saduwa, kiyi amfani da condom domin taimakawa wajen rage yaduwar cutar ta sanyi.

Rage Amfani da Sabulu Mai Karfi: Amfani da ruwa kadai musamman mai ɗumi wajen wanke farji yana bada kariya sosai.

Shan Ruwa Mai Yawa: Shan ruwa da yawa yana taimakawa wajen wanke mafitsara daga kwayoyin cutar.


A Tuntubi Likita

Idan kin gwada yadda ake hada maganin sanyi, gargajiya ko zamani amma alamun sanyi ko ita kanta cutar basu rabu dake ba, hakan zai iya faruwa ne sakamakon sanyin ya yi tsanani, to ina bada shawara yana da kyau ki gaggauta zuwa asibiti. Alamun daya kamata ki sanya hankalinki a kansu, sun hada da:

Zafi musamman yayin fitsari.

Fitar ruwa mai wari daga farjinki.

Zafi mai tsanani a cikin ciki.

Jin kasala ko zazzabi mai tsanani.


Tambayoyi da Amsoshi Akan Cutar Sanyi

Shin maganin sanyi na gargajiya ya fi tasiri?

Eh, Wannan haka yake, domin gaskiya maganin gargajiya yana da tasiri sosai ga cutar sanyi, musamman idan anyi amfani da shi bisa ka'ida yadda ya kamata. Amma idan matsalar tayi tsanani, likita zai iya bada tasa gudummawar ta hanyar amfani da magungunan asibiti.

Za'a iya amfani da kayan gargajiya da na asibiti a lokaci guda?

Gaskiya a shawararce kar kiyi haka, sabida yana iya haifar miki da matsala ko rashin lafiya wacce bata da dalili. Ki tuntubi likita ko Malama kafin ki hada kayan gargajiya dana asibiti.

Shin zuma da lemon tsami na iya magance dukkan nau’in sanyi?

A'a, zuma da lemon tsami suna taimakawa ne wajen kashe bacteria ko kuma sanyi wanda bai yi nisa a jiki ba. Amma Idan matsalar ta shafi mahaifa ko mafitsara, akwai bukatar karin wasu magunguna.

Ayi sani cewa maganin sanyi na budurwa ko namiji ya dogara ne da nau’in sanyi dake damunki ko yake damunka, domin kowane nau'i da nasa irin maganin, wanda aka fi amfani dashi. Amfani da kayan maganin gargajiya kamar zogale, kanumfari, da tafarnuwa nada matukar tasiri wajen magance wannan cuta ta sanyi. Amma idan matsalar ta tsananta, zai fi kyau a tuntuɓi likita domin samun magani mafi inganci. Ki tuna, tsafta da kula da jiki su ne abubuwa mafiya muhimmanci wajen kare lafiyar ki daga cututtukan sanyi.