Hanyoyin samun ciki ko ya ake yiwa mace ciki
Yau kuma ga wata sabuwa wato yadda ake daukar ciki, dama wasu jawabai na alamomin shigar ciki a satin farko, ko hanyar samun saurin daukar ciki.
Yadda ake daukar ciki na musulunci:
Wannan rubutun ƙunshe yake da step by step watau daki daki na matakan da suke faruwa ko kuma suke kasancewa kafin ciki ya samu a jikin mace.
A ƙiyasce hukumar lafiya ta duniya tayi ittifaƙin duk bayan minti ɗaya ana samun shigar ciki a jikin mata a ƙasar Najeriya.
Saduwa watau jima'i wani ginshiƙi ne a tsakanin jinsin namiji da mace wanda amfaninsa ko muhimmancin sa ba zai misaltu a kalamai na fatar baki ba. Aure dai ana yinsa ne domin a hayayyafa a samu zuri'a ko kuma a samu ƙaruwa. Ta hanyar jima'i ne kawai watau saduwar namiji da mace jinsin ɗan adam zai cigaba da yaɗuwa a doron duniya.
A wannan zamanin dai da muke ciki ilimin kimiyya da fasaha watau science and technology yazo da wasu dabaru da akeyin dashen maniyyin namiji a cikin mahaifar mace ta É—auki ciki ba tare da saduwa tsakanin jinsin biyu ba, watau surrogacy a turance to amma mafi gamsuwa dai itace ta hanyar tarawa tsakanin jinsin biyu watau ta hanyar jima'in, domin itace hanya natural kuma mafi gamsuwar yaÉ—uwar É—an adam.
Ba samar da yaɗuwar jinsin kawai ba, jima'i yana da amfani sosai ga jikin ɗan adam kamar rage urge na sha'awa a wurin baligi namiji da baliga mace, kamar sha'awa da ke damun samari da ƴan mata, samar da nutsuwa ga kwakwalwa, ƙara ƙarfafa garkuwan jiki da kuma daidaito a tsakanin sinadaran dake jikin dan adam.
Sassan jima'i a jikin dan adam;
Sassan jima'i wasu gaɓoɓi ne a jikin mutum da ake amfani ko kuma suke taimakawa wajen yin jima'i. Waɗannan sassa sun bambanta tsakanin mace da namiji.
Sassan jima'in namiji:
Male reproductive organs
Penis : Azzakari
Testes :Ƴaƴan maraina
Scrotum : Fatar da ke É—auke da Æ´aÆ´an marina
Urethra : Bututun da ke fitar da fitsari da ruwan maniyyi
Sassan jima'in mace
Vagina : Farji
Uterus : Mahaifa
Ovaries : Gland ne dake samar da ƙwai a duk wata (month)
Fallopian tubes: Bututu ne dake ɗaukar ƙwai daga ovaries zuwa cikin mahaifa
Clitoris : Dan tsele, dan tsaka ko kuma beli
Labia majora : Laɓɓan farji manya
Labia minora : Laɓɓan farji ƙanana
Hymen : Tantanin budurci, yana fashewa da zarar aka fara jima'i da mace.
Yadda ake tsokano sha'awa:
Kamar yadda wata doka watau (law) take bayyanawa a cikin ilimin fiziya (Physics) da take cewa: like charges repel, unlike charges attract.
Kasancewar jinsin biyu na namiji da mace suna da bambancin halittu musamman a tsarin reproductive system watau a halittun su na jima'i. Kasancewar wannan bambance bambancen dake tsakanin sune asali kuma silar sha'awar dake ginuwa tsakanin jinsin biyu. Namiji yana sha'awar abinda yake hanga ko kuma yasan cewa mace ta mallaka a jikinta yayin da mace take sha'awar abinda namiji ya mallaka a jikinsa. Idan munyi duba zamu ga cewa ko a tsarin halayyar ɗan adam mutum sau tari yafi hangowa da kuma hasosawa kansa abinda waninsa ya mallaka koda kuwa shi abinda ya mallaka yafi na wanin nasa ƙima da daraja.
Me ke sa azzakarin namiji ya miƙe a lokacin sha'awa?
Da farko a duk lokacin da sha'awar ɗa namiji ta motsa to akwai alhakin wani tsari na jiki wanda dashi ne kwaranyar jinin jiki take gudana watau circulatory system a turance, shine zai taimaka wurin karkatar da jini zuwa azzakarin namiji a yayin da sha'awa ta bijiro masa. Azzakari yana ɗauke da jijiyoyin jini da wasu tsokoki na musamman waɗanda zasu iya ƙara tsawo kuma zasu iya ragewa. Hakan zai nuna mana cewa a tsarin halittar azzakarin da namiji akwai elasticity wanda hakan ne ke sawa azzakarin ƙanƙancewa ko kuma yayi girma, kauri da tsayi a wasu lokutan kamar lokacin sha'awa.
Ta yaya namiji yake yin releasing watau inzali ?
Jin daɗin jima'i da farko kai tsaye ba daga haɗuwar jikin jinsin namiji da mace bane ko kuma taɓe taɓen jiki ko kuma wasanni da jikin junansu. A'a, kafin a samu wannan jin daɗin na haɗuwar sassan jiki kamar taɓa nonon mace daga wurin namiji ko wasa da azzakarin namiji daga ɓangaren mace sai kwakwalwa ta fara ɗaukan wani abu da ake kira da "stimulus" watau canji ko kuma baƙon lamari a jikin ɗan adam daga kuma wani jakadan na kwakwalwa mai suna "receptor". Sannan ne kwakwalwa zata fassara shi ga ragowar sassan jima'i kamar azzakari, farji, nono da dai sauransu. A cikin ire iren wannan jin daɗin da kwakwalwa zata fassara ne ake samar da gamsuwa watau ejaculation, releasing ko kuma a yaren hausa muke cewa inzali. Wanda a shine namiji yake samar da kwayoyin ko kuma kwan halittarsa a cikin maniyyi watau sperm ko kuma semen.
Kamar yadda bincike a ilimin kimiyya ya tabbatar wannan maniyyi na da namiji a duk fitowa daya yana samar da kimanin miliyan talatin da tara zuwa miliyan É—ari biyu(39 - 200 millions) ga cikakken namiji mai lafiya. Duk yawan waÉ—annan kwayoyin halittar kuma guda É—aya ne kacal zai samar da ciki bayan shiga mahaifar mace.
Abin lura: a lokacin da namiji yake cikin ƙaramar sha'awa kamin ya fara jima'i ko lokacin da ya ke tunanin saduwa, ko lokacin wasanni na soyayya da mace to azzakarin namiji yana samar da wasu ruwa marasa kauri wanda a hausan ce akafi sani da ruwan maziyyi shi wannan ruwa shine pre seminal fluid. Kuma fitar wannan ruwa alama ce ta cewar babbar sha'awarta ɗa namiji na nan tafe bada jimawa ba.
Yadda ake tsokano sha'awar budurwa ko duk wata mace
Shafa, tsotsa matsa ko kuma shinshinan wasu sassa na jikin mace sune suke haɓɓaka ruruwar sha'awarta . A lokacin da sha'awar mace ta motsa ƙwaƙwalwar zata karɓi saƙon stimuli watau canji ko baƙon al'amari kamar yadda na bayyana a sama ta hanyar ɗan aikenta watau receptor haka zalika ƙwaƙwalwarta zata yi umurni ga wasu glands da ke cikin mahaifarta su fara samar da wasu ruwa masu yauƙi, waɗannan ruwan sune zasu gangara zuwa farjinta domin su samar da ni'ima, da santsi a lokacin da fatar azzakari ke taɓa fatar farji. Kamar dai namiji ita ma mace fitar wannan ruwan daga farjin ta alama ce dake nuna babbar sha'awa na tafe bada jimawa ba.
Yadda mace ke inzali idan taji daÉ—in jima'i
Fitar da wannan ruwan dana ambata a sama daga cikin mahaifa shi ake kira da inzalin mata ko fitar ruwan maniyyin mata. Haka kuma fitar wannan ruwan yana kai maƙura ne a lokacin da mace ta kai maƙurar jindadin jima'i.
Abin lura, shi wannan ruwan da ke fita daga farjin mace a lokacin da ake jima'i da ita har yanzu yana cikin babin mahawara ne a wurin masana ilimin kimiyyar ɗan adam. Saɓanin ruwan maniyyin da ke fita daga azzakarin namiji a lokacin jima'i, shi ruwan maniyyin da ke fita daga farjin mace aikinsa kawai shi ne samar da ni'ima da santsi da kuma inganta jindaɗi na musamman a lokacin saduwa.
Ya mace ke bada gudunmawa wajen samun ciki (juna biyu)?
Mace tana bada gudunmawa ne ta hanyar samar da wani Æ™wai dake fitowa daga ovaries dinta. A duk wata (month) mace tanayin Æ™wai a cikin ovaries nata wanda yana samuwa ne a tsakiyar watan ta na al'ada. Hakan zai yi dai dai da rana ta goma ko ta sha É—aya zuwa ta sha huÉ—u bayan tayi tsarki daga jinin al'ada. Samar da kwai a jikin mace ya samo asali ne idan har ta balaga koda kuwa ba'a taba yin jima'i da ita ba, saboda haka samuwa kwai a jikin mace sam bashi da alaka da jima’i.
Yadda ake É—aukar ciki (shigar ciki a jikin mace)
A duk lokacin da mace tayi ƙwai ta fitar dashi ya kan fito daga ovaries dinta zuwa mahaifarta. Idan ta samu nasarar yin jima'i a lokacin da ƙwan yake da rayuwa (ƙwan ya kan ɗauki kwana biyu zuwa uku kamin ya mutu) har ruwan maniyyin namiji suka zuba a cikin farjin ta, toh tantanin halittun haihuwar da ke cikin ruwan maniyyin namiji zasuyi rigaye domin suje cikin mahaifarta su sadu da ƙwan domin a samu ciki.
Kwan halitta na mace yana samuwa ne a matsayin sabo bayan kammala jinin al'adar ta. A yawancin mata yayin duk da suka kammala jininsu na al'adar to kuma akwai wani ruwa da yake fitowa bayan jini ya É—auke. Wannan shine abinda ake kira da ovulation a turance, kuma mafi akasari idan namiji ya sadu da mace a wannan yanayi na ovulation to akwai chance ko kuma dama tacewa wannan matar zata samu ciki ko kuma ta dauki ciki a kaso saba'in cikin dari. (70/100). Ilimin kimiyya ya tabbatar da wannan a bincike.