Yadda ake saduwa da mace uwargida post
Wacece uwargida ne ma dai tukunna?
Uwargida dai itace wannan matar da hausawa sukan yiwa kirari da sarautar mata. Ga mazaje da yawa, uwargida itace wannan matar ta lalle, tsohuwar zuma kenan wacce ake magani da ita. A taƙaice dai uwargida itace amanar maigida domin kuwa itace tafi sanin sirrikan maigida. Idan har maigida bai kyautatawa uwargida ba, to shi kuwa maigida wa yake ganin yafi cancanta daya kyautatawa?
A kullum ta duniya maza ma’aurata suna saduwa da matansu, sai dai kuma abun tambaya anan shine, maza nawa ne suke iya gamsar da matayen nasu a lokacin da sukayi kwanciyar jima’i? Maza nawa ne magidanta suke da illimin sanin yadda zasu gamsar da matansu? Ko munki ko munso babu yadda zamu kaucewa magana a kan jima’i domin shine ginshiÆ™in zaman aure kuma yana cikin manyan lamuran da kan iya sa a samu zaman lafiyar ma’aurata ko akasin hakan.
Saduwa da mace a kuma gamsar da ita, ba ƙaramar kyautatawa iyali bace bafa, sai dai abin ban haushi ga maza, haka kuma abin ban tausayi a wurin mataye, mazajen da basa gamsar da matansu suna nan da yawan gaske a doron duniya. Irin mazajen nan fa sun zaci cewa da sun kwanta da matarsu sun samu gamsuwa shikenan ita kuwa iyalin tasu ko oho. Wannan ba ƙaramin rashin adalci bane, haka kuma yana da illolinsa masu yawan gaske.
Yana da kyau da kuma mahimanci maza su fahimci cewa, duk wata mace tana sha’awar ganin cewa mijinta yana matuÆ™ar gamsar da ita yayin da suka yi kwanciya ta jima’i. Sai dai kuma abun ban haushi maza da dama suna É—auka cewa gamsar da mace a jima’ince shine saduwa da mace da Æ™arfi ko kuma da mugunta ko jigatata shine zai iya gamsar da mace.
Mafiya yawan maza basu da ilimin sanin cewa mace takan ɗauki lokaci mai tsawo kamin tayi zuwan kai ma'ana kafin ta kawo, duk da yake da akwai wasu matan da suke yinsa cikin ƙaramin lokaci. Don hakane yake da kyau maza su gabatar da wasanni ga mace kamin su afka mata.
Kamin mace ta kamu, dole ne sai an tattaÉ“a mata wasu wurare ta hanyar sumbata, wasa da nonuwanta, gabanta da makamantan su. A wannan lokacin ne mace jinin jikinta yake bin ko ina a jikinta daga nan kuma sha’awa ta motsa mata harta nemi buÆ™atar mijinta.
Muddin namiji ya jefa matarsa cikin wannan yanayi zai ji daÉ—in yin jima’i da ita haka kuma ita kanta matar ba zata yi kukan rashin gamsuwa bayan an gama ba, maza masu murza matayensu a lokacin wasannin motsa sha’awa, mazane da suke sa matansu gamsuwa da zuwan kai cikin sauÆ™i kuma akai akai.
Muna magana ne akan yadda ake saduwa da uwargida ko? To maza ku bani aron hankulanku da kunnuwanku na baku wani sirri. Ita fa uwargida itace macen da zaka iya gamsarwa cikin sauƙi ko da kuwa kai baka da buƙatar yin abin, a yayin da ita kuma take a buƙace, take kuma son ayi abin. Uwargida matarka ce da kuka jima tare, don haka ya kamata ace ka riga ka fahimci ita ɗin wace iriyar mace ce a fagen shimfiɗa.
Kada kayi gaggawar shigar uwargida watau matarka a yayin daka É—aura niyar kwanciya da ita, ka tabbatar ka É—auki lokacin kamar mintuna 25 zuwa 30 kana wasa da ita har sai lokacin da tayi laushi da kanta tana buÆ™atar ka shigeta. Mata da dama dai sukanyi sha’awar ganin mazansu ne ke tuÉ“e su da kansu a lokacin da ake tsaka da wasan, yadda kuma a yayin wasan kana tuÉ“e mata kayan dake jikinta É—aya bayan É—aya kafin ka shiga wasa da muhimman wuraren dake motsa mata sha’awa.
Da yake bazan yi bayani dalla-dalla na yadda ake wasa da mace da kuma wuraren da ake wasan dasu ba a wannan rubutun, yana da kyau maza su fahimci cewa ko wace mace da inda ke tayar mata da sha’awarta. Wata da zaran an soma shan bakinta sha’awarta zata motsa, irin waÉ—annan matan sha'awar su akan gaÉ“a take, saboda basa É—aukan lokaci mai tsaho sha'awar su take zuwa, wata kuma wasa da gabanta, irin matan dake É—aukan lokaci kafin zuwan sha'awa kuma basa kawowa da wuri. Wata murza kan nonuwanta wata ma kunnenta kawai za’a taÉ“a ta fara É—iga, dole ne kowane magidanci ya fahimci meke tayarwa da matarsa sha’awa a lokacin wasanni. Kamar yadda na faÉ—a muku a sama, uwargida tafi kowace mace sauÆ™in gamsarwa idan har maigida yasan hannunsa.
Mahimmancin wasa da uwargida kafin soma jima’i shine, zai sata ta soma fitar da ruwa wanda ruwan yana taimakawa shigar azzakari cikin farjin mace da sauÆ™i. Haka kuma yana taimakawa mace tayi zuwan kai cikin sauÆ™i ba tare da ta É—au lokaci ba.
Girman azzakari, ko tsayinsa bashi ne abu mafi mahimmanci ba a wajen mace, abun da kawai yake sa mace ta samu zuwan kai da kuma gamsuwa a yayin jima’i, shine yadda aka motsa mata sha’awarta a lokacin da ake wasa da ita, shine abunda yake sata nan take ta samu zuwan kai da kuma gamsuwa irinta jima’i.
Babu saduwar jima’i mafi daÉ—i wajen mace irin tayi zuwan kai lokaci guda da mijinta, wanda bincike ya nuna cewa a maza 100, 40 ne kawai suke iya yin zuwan kai lokaci É—aya da matansu, hakan kuma yana samuwa ne ganin yadda suka laÆ™anci jima’i da matan nasu. Wannan ita kaÉ—ai ce hanya babu tsimi babu dabara.
Shi dai zuwan kai na Æ´a mace, shine Æ™ololuwar jin daÉ—in kwanciyar jima’inta, kuma shine yake jawo gamsuwarta a jima’ince, don haka da zaran wasu matan sun samu gamsuwa to sha’awarsu ta jima’i kuma ta Æ™are a wannen lokacin, duk kuwa da wasu matan da ake samunsu suna iya zuwan kai kamar sau biyu zuwa biyar a kwanciyar jima’i guda, hakan yana danganta ne da irin halittar macen da kuma yadda mijinta yake sarrafata a jima’ince.
Shi dai zuwan kan Æ´an mace ba kamar na namiji bane, domin shi namiji idan yayi zuwan kai abune da ake iya ganinsa a zahiri saboda yadda maniyi yake fita daga azzakarinsa. Wasu na É—aukar cewa, ruwan dake fita daga gaban mace a lokacin saduwa da ita shine zuwan kan nata, (duk kuwa da akwai matan da suke kawowa yadda maza keyi) abun ba haka yake ba.
Ruwa iri biyu ne yake fita a gaban mace a lokacin da ake wasa da ita wani ruwa mai yauƙi ne yake soma fitowa, wanda yake alamta cewa ta soma kamuwa kenan, haka kuma idan ana saduwa da ita kuma da akwai wani farin ruwa wanda yafi kama da madara shima yana fita daga gabanta, shima wannan bashi ne alamar mace tayi zuwan kai ba.
A lokacin da mace tazo kawowa, a wannan lokacin kamanninta sukan canza, numfashinta yana yawan bugawa da sauri, haka kuma jinin jikinta gudun sa na ƙaruwa sosai haka kuma jijiyoyin jikinta zasu ƙara bayyana yayin da zata yi wata ƙara ko kuka ko faɗar wata kalmar da bata santa ba a yayin zuwan kan nata, haka kuma mata da dama suna ƙanƙame mazajensu a lokacin da suke zuwan kai.
Sai dai kuma kafin wannan lokacin, ya kamata maza su fahimci cewa da akwai illa ga duk namijin da bazai iya gamsar da matarsa ba a jima’ince, don haka ne nake bada shawara ga maza su nemi sanin illimin yadda zasu iya sarrafa matansu.
Kar ku manta, naƙaltar irin halittar matayenku a wurin jima'i shine babban sirrin hanyar da zaku bi wurin gamsar dasu.