Yadda ake gane anci budurwa ko mace article#
A yau maudu'in namu zaiyi dogon nazari da cikakken bayanin yadda zaku gane shin anyi amfani da mace, ko kuma an taɓa amfani da ita, ko kuma ana yin amfani da ita, budurwa ce ko bazawara, koma dai a wani rukuni wannan talikar ta faɗo, wannan rubutun zaiyi bayani ne akan duk wasu alamomi da kuma sauye sauye da zaku gani a tattare da ita, wanda idan kuka lura dasu to zaku gane cewa eh! Anyi abin ko kuma ana yin abin da ita.
Kafin na shiga bayani gadan gadan akan yadda zaku gane cewar an taɓa amfani da budurwa ko wata mace, ko kuma ana amfani da ita, yana da kyau ku fara gane cewar duk abubuwan da za'a karanta a cikin wannan rubutun ko kuma nace duk abun da rubutun nan zai ƙunsa ya karantar daku, tofa babu guarantee na cewar idan kunga hakan daga cikin abubawan da zan lissafo akan budurwa ko kuma wata mace, to baya nufin cewa lallai anyi amfani da ita, ko kuma ana amfani da ita, ko kuma an taɓa amfani da ita. Ku riƙe wannan!
Duk wasu alamomi da wannan rubutun zaiyi bayani na yadda zaku gane hakan, tofa babu tabbas ɗari bisa ɗari sai dai zai zamanto kamar wani analysis da buɗewar ido haɗe da ankarar daku, na yadda zaku iya ganewa hakan, kunsan hausawa masu iya magana suna cewa; labarin zuciya a tambayi fuska, to kamar haka ne.
Gare ku ƴan mata, matan aure da samari ya kamata kusan waɗannan hanyoyi na yadda ake iya gane an taɓa amfani da budurwa don zai iya amfanar daku. Domin kuwa ba kasafai ake iya ga ne budurwa ta rasa budurcinta ba, sai wanda ya karanci yadda ake iya gane hanyoyin.
Samari da dama na son sanin budurwar da zasu aura cikakkiya ce ko kuwa wani ya taɓa kwanciya da ita yayi amfani da ita. Da yawa yawan samari na shiga irin waɗannan tunanin da shakku a zukatansu, hakan yasa wasu ke fara tunanin yadda zasu gano budurwar da zasu aura cikakkiya ce ko akasin hakan.
A bincike da yawa an gano cewa a zamanin yanzu da wuya ka samu saurayi da budurwa kafin suyi aure basu taɓa ɗanɗana daɗin jima'i ba. Sai dai su samari suna ganin hakan a wajen su ba wani abu bane. Saurayi yana iya neman budurwa yayi amfani da ita amma kuma shi ba ya son a yiwa budurwar da yakeso ya aura.
Kamar yadda samari ko mazan dake son auren budurwa ke neman sanin shin an taɓa amfani da ita ko kuwa ba a taɓa yi ba. Gaskiya dai iya bincike babu wasu hanyoyi ko alamomi na zahiri da za'a iya gano cewa budurwa ta taɓa yin zina idan har ba ita ce ta bayyana maka ba, ko kuma idan ka aureta ka gano hakan. Amma kamar yadda na ambata a sama duka hanyoyin da zanyi bayani a yanzu, zasu buɗe muku idanu ne haka kuma zasu saku a hanya su ankarar daku wurin gane duk abinda kuke son ganewa game da hakan.
Da farko dai, ku sani duk wasu alamomi da za'a tattauna sun danganta da dabi'un ita macen ko kuma budurwar da ake son gano ana amfani da ita ne ko ba'a yi. Hakan ya samo asaline tunda dai babu wata hanya da za'a iya gane hakan sai a mu'amala ta yau da kullum.
Wasu daga cikin hanyoyin yadda ake gane anci budurwa ko mace hakan sun haɗa da;
1- Ita budurwar ko kuma ita macen ta faɗa da bakinta cewa eh, ana amfani da ita ko kuma an taɓa amfani da itan. Babu wata hanya data kai wannan sahihanci da kuma tabbacin cewar ana amfanin da ita. Amma matsalar itace, yiwa budurwa irin wannan tambayar ba ƙaramin ganganci bane, tunda idan kayi mata irin wannan tambayar to kuwa lallai zaku kwashi ƴan kallo da ita, ƙila ma idan ba ayi sa'a ba, ƙarshen alaƙar kune zai zo sakamakon wannan tambayar gangancin da kayi mata.
A maimakon hakan, sai a gujewa yin irin wannan tambayar ta kai tsaye haka kuma ta ganganci. Duk mai son gane irin wannan batun sai yafi maida hankali akan sauran hanyoyi da kuma alamomin da wannan rubutun zai cigaba da bayyanawa kamar haka;
2- Ana iya gane cewar ana amfani da budurwa ta nonuwanta, yayin da aka ga nonuwan nata sun matuƙar cika ƙirjinta taf. Koda yake, wasu matan da yawa yanayin halittar sune hakan, watau cikar ƙirji, amma duk yarinyar ko budurwar da kuka ga a farkon al'amari bata da cikar ƙirji amma kuma kwatsam sai aka wayi gari ƙirjin nata ya soma cika yana ƙara girma fiye da misali to da walakin goro a miya. Walau ana taɓa mata ƙirjin ne kawai ana wasa dashi, walau kuma ana taɓa mata shine a yayin da ake amfani da ita. Koma dai wanne ne, wannan hanyar na ɗaya daga cikin hanyoyin da zaku riƙa ankara dasu.
Cikar ƙirjin nata zai kasance ne yadda duk wani namiji mai lafiya in yayi mata kallo ɗaya yayin da take tafe ƙirjinta na gaba sai yaji wani abu ya ɗarsu a zuciyar sa. Irin wannan cikar ƙirjin na alamun tambaya ne, kamar yadda na bayyana, musamman idan kun san cewa da farko bata da cikar ƙirjin.
3- Ku lura ku gane kuma duk budurwar da aka saba amfani da ita bata tsoron maza ko kunyarsu, domin babu wani abu da bata gani ba ko bata sani ba a game da shi namijin kansa. Wannan ne dalilin. Saboda haka in dai ka fahimci budurwarka haka take, to a cikin ɗaya biyu; ko dai a cikin yayye da ƙanne maza ta taso ko kuma an taɓa kwanciya da ita.
Wannan rashin kunyar da rashin tsoron ya samo asali ne, saboda ta riga ta san ɗa namiji, ma'ana tasan sirrin namiji. Tasan komai kenan. Shiyasa za kaga bata kunyar ka ko shayinka, itama wannan wata alama ce da zaku saka ta a cikin irin wannan lissafin naku, a ƙoƙarin ku na gano idan an taɓa amfani da budurwa ko kuma ana amfani da ita, muje zuwa.
4- Kallo, eh kallo nake nufi. To amma wane irin kallo? Kallo kala kala ne, irin kallon da nake nufi anan shine ba wai ta kalle ka sau ɗaya sau biyu ba, a'a. Wani irin kallo ne wanda ba normal ba, za kaga yarinya ta ƙurawa cikin kwayar idanunka ido, kamar yadda na bayyana a sama. Kallo ne wanda kai kanka wanda ake yiwa sai ka tsargu. Kuma shi wannan kallon, kallone wanda yake psychologically ne, yarinyar ko kuma nace budurwar take aika maka. Ba lallai ne lissafin da zan bayyana maka ya kasance haka ba, amma dai bayan na bayyana maka zaka fi hasaso abin da nake nufi.
Wannan irin kallon ƙurillar daza kaga budurwarka nayi maka, tana hasaso yadda zaku kasance ne, kamar yadda ta kasance da waninka, ko kuma yadda take kasancewa da waninka, wannan shine lissafin yawancin irin matan nan masu yiwa maza irin wannan kallon. Ba kallone na sha'awa ba, kallo ne na hasashe ko kuma tu'ajjibin yadda zaku kasance tare.
Karka fara tunanin cewar ana amfani da yarinyar kawai don tayi maka irin wannan kallon sau ɗaya. Amma idan kaga yarinya ta fiye yi maka irin wannan kallon sau tari, to kasa lissafinka da kuma ayar tambayar nan, ta ko namiji ya santa a cikin lissafinka.
5- Hanya ta biyar a cikin wannan rubutun itace idan kaga budurwarka ko kuma kaga yarinya bata tsoro ko kuma kunyar kusancinku wurin zama. Ko kuma yarinya bata shayin zama kusa da namiji har kusancin nasu yayi yawa. Duk mace da zata zauna da namiji kafaɗa da kafaɗa kuma ya zamana ba tilasta mata akayi ba, to ka ɗora ayar tambayarka akanta. Mace wacce bata san namiji ba, ba zata so ko kuma ba zata yarda da zama daf da namiji ba, ko da saurayinta, sai dai idan soyayyar shan minti sukeyi.
Saboda haka idan kaga yarinya bata gudun ku zauna da kusanci sosai to da walakin, domin kuwa idan har kuka zauna kusa da kusa da yayinyar to kuwa abinda zai biyo gaba shine fara taɓa sassan jikin juna, idan kuwa hakane to kaga kuwa ba abin mamaki bane idan nace maka hakan na ɗaya daga cikin manya manyan alamomin cewa ana amfani da ita wannan budurwar ko yarinyar, domin haka kasa hakan a cikin lissafinka matuƙar kaga budurwa ko yarinya ko kuma wata mace bata shayin zama akusa ko kuma a jikin namiji.
6- Idan budurwarka, ko yarinya ko kuma kaga mace ta cika chaɓa kwalliya sosai koda ba biki za taje ba, kuma irin wannan kwalliyar daza kaga ana saka sutura mai bayyana sura ko tsiraicin jiki, kwalliyar tata ta kasance tana tayar da hankalinka, ma'ana tana tayar maka da sha'awarka, to hakan wasu alamu ne dake nuna wannan yarinyar ta ƙuna, kuma abokin mutuwa take nema. Yarinyar da bata san daɗin namiji ba zaiyi wahala ta riƙa irin wannan shaiɗaniyar kwalliyar tana saka yankakkun kaya masu nuna sassan jikinta, wanda hakan duk yana daga cikin alamun ana yin abin da ita. Ku saka wannan a cikin lissafin ku na yadda zaku gane shin ana amfani da budurwa ko ba'a yi.
7- Idan ya kasance kai da budurwar taka kunayin soyayyar minti ne, har ya kasance idan kuna shan minti kaga ta kware sosai a ire iren wasannin da kuke yi, musamman idan ana taɓa sassan jikinta, kuma hakan baya sawa jikinta ya riƙa kyarma ko kuma idan ana taɓa ta, jikin nata ya riƙa rawa kamar an saka mata shocking, da zarar kaga haka to wannan ma wata alama ce dake nuna budurwar ko kuma yarinyar ta saba da maza. Hakan tabbas wata babbar alama ce manuniya dake nuna tana wasa da namiji ko kuma tana wasa da maza, kuma wannan babbar alama ce ta ana amfani da ita budurwar.
8- Haka kuma idan kaga a ire iren wasannin shan mintin nan naku ka lura kaga ta iya wasannin nan sosai, misali idan kaga cewa duk wannan kiss kiss din da rungumar juna da zaku keyi, kaga ta kware sosai tasan duk yadda akeyi, harma kana ganin cewa ba zaka nuna mata kwarewa a wannan fannin ba, to gaskiya idan kaga budurwarka na haka, to abune mawuyaci kaga ba ƴar hannu bace, ma'ana dai ƴar harka. Duk macen da ta iya irin waɗannan wasannin har ma ta kai ga kwarewa a wasannin tofa zaiyi wuya ba'a amfani da ita. Macen da idanun ta basu buɗe ba, babu yadda za'ayi ta iya irin waɗannan shu'uman wasannin har ta kai ga kwarewa sosai.
Kamar yadda na bayyana a farko, duka waɗannan hanyoyi ko alamomin da aka karanta wanda kuma za'ayi nazari akansu, ba lallai bane su tabbatar da hasashen mai karatu akan zarginsa da yake akan budurwa ana amfani da ita ko ba'a yi
Sai a kiyaye!
Yadda ake gane anci budurwa ko mace article end#