Alamomin shigar ciki a satin farko post#

Abu ne mai muhimmanci kowace mace ta san alamomin dake nuna shigar ciki, sa'annan ta fahimta idan taji kota ga waɗannan alamomin dake nuna tana ɗauke da sabon ciki.

Bayyanar ciki a jikin mace bayan aure abin farin ciki ne ga mata da yawa, tare da mazajensu, amma zai iya zama kuma wani abu mai wahala da kuma damuwa. Wasu daga cikin abubuwan da mata da yawa basu sani ba shine alamomin da zasu lura dasu su fahimcesu su ganesu dangane da shigar ciki a satin farko. A wannan maudu'in, zanyi bayani na wasu daga cikin alamomin da mata zasu iya ganewa a satin farko na shigar ciki. 

Wani bincike ya gano cewa da yawa daga cikin mata idan sun samu ciki ba kasafai suke ganin wasu alamomi a satin farko ba, amma wasu suna ganin alamomin kamar rashin lafiya, ciwon nono, da kuma ciwon ciki mai nauyi a cikin kwanaki 5-6 bayan jima'i. Wannan ɗin alamar shigar ciki ce a satin farko. 

Masana ilimi na lafiya sun bayyana cewa mata suna iya gane shigar ciki a satin farko idan suka yi la'akari da yin al'adar su ta ƙarshe. Amma wannan maudu'in kamar yadda na bayyana a sama zaiyi bayanin alamomi na zahiri da mata zasuyi saurin ganewa.

Alamomin shigar ciki a satin farko
Alamomin shigar ciki a satin farko post#

Missing kwanakin yin period watau al'ada, shine babbar alama ta farko da mace zata iya gane ta samu ciki. Wasu daga cikin alamomin shigar cikin na satin farko sun haɗa da:

_Ciwon ciki 

_Canjin nono; kamar ciwon nono, kumburin nono ko kumewar nono.

_Tashin zuciya da jin alamun kumallo 

_Yawan sha ruwa

_Yawan fitsari

_Ciwo kai

_Kumburin ciki da yin gyatsa 

_Rashin lafiya ko rashin ƙarfin jiki

_Zargi ko canji a halin zuciya

Yana da muhimmanci a lura cewa ba a fiya ganin waɗannan alamomin shigar ciki a satin farko ba. Hanya mafi sauki da mace zata gane tana da juna biyu shine taje ai mata gwaji a asibiti.

A ƙarshe, makon farko na shigar ciki shi ne lokaci mai muhimmanci ga mai cikin da kuma abinda ke cikinta. Yayin da yawan mata basu ganin wasu alamomin gane suna da ciki a wannan lokacin, wasu kuma zasu iya samun alamomin shigar ciki kamar rashin lafiya, ciwon nono, da kuma ciwon ciki mai nauyi. Idan kuka ji wannan alamomin zai iya yiwuwa shigar cikin ne, yana da muhimmanci kuje kuyi gwaji tare da neman shawarar data dace daga wajen likitoci.

Tun kafin kije asibiti a gwada ki, a tabbatar kina ɗauke da juna biyu ko akasin haka, to yana da kyau ki san ta yadda zaki gane kina ɗauke da cikin ta yadda za kije da kwarin gwiwarki.

Babban abin dake kawo ɓatan wata shine samun juna biyu.Bayan juna biyu kuma cututtukan shigar kwayoyin cuta mahaifa sune kan gaba wajen kawo batan wata, ko rikicewar lissafin wata. Sauran sun haɗa da shayarwa, yawan damuwa ko ciwon damuwa, da rashin zama wuri ɗaya ko rashin samun hutu.

Shin mace zata iya gane tana da ciki kafin zuwa asibiti?

Kwarai zata iya, amma kamar yadda abin yake, bafa kowace mace ce tasan cewa ɓatan wata shine babban abin dake kawo juna biyu ba.

Sannan kwayoyin cuttukan dake shiga mahaifa suma suna kan gaba wurin kawo ɓatan wata [wato rashin ganin al'ada], ko kuma rikicewar lissafin wata.

Karin abubuwan dake kawo rashin ganin jinin al'ada sun haɗar da:

Rashin zama wuri ɗaya

Shayarwa

Rashin samun hutu [sakamakon yin wasanni masu tsanani]

Fama da ciwon damuwa ko yawan ta

Haka kuma a lokuta da dama shan magunguna barkatai walau na gida ko na asibiti, to suma suna iya haifar da ɓatan wata.

Abubuwan nan biyar dana jero, sune waɗanda binciken likita ya bayyana suna haifar da matsalar rashin ganin jinin al'ada.

Duk da bayan su kamar yadda aka bayyana a baya, shigar kwayoyin cuta cikin mahaifa da samun juna biyu su ma suna iya haifar da ɓatan wata.

Yanzu kuma za mu gangara kan alamomin ciki daga satin farko.

Alamomin ciki tun a satin farko na aure:

Yayin da ciki ya shiga, a satin farko mafi akasarin mata basa fuskantar ko ganin wata alama ta ciki ya shiga jikinsu. Sai dai duk da haka wasu matan na iya ganin wasu alamomi dake nuna shigar cikin da wuri kamar haka:

Zubar jini

Wani irin zubar jini ne dake faruwa kwanaki 10 zuwa 14 bayan ɗaukar ciki, kuma yana aukuwa ne bayan kwayar halittar manin [da za'a halitta] ya manne da rufin mahaifa.

Kumewar nono: Mace za taji nononta ya kumbura ko ya kume.

Gajiya: Mace za taji gajiya fiye da yadda ta saba jinta.

Sauyin yanayi: Mace za taji yanayinta na saurin sauyawa [ko dai tana yin saurin fushi].

Ƙamshi: Ko kuma mace taji tana jin ƙamshi [koma wanne iri ne] fiye da yadda ta saba.

Duk macen da taji a satin farko tana fuskantar ko jin irin waɗannan alamomi to yana da kyau taje asibiti domin ayi mata gwajin ciki domin ta tabbatar da cewa tana da shi ko a'a. 

Rashin ganin al'adarki da wuri ba shine farkon alama cewa kina ɗauke da ciki ba. Akwai alamomi da yawa dake nuna kafin lokacinki na al'ada yayi. Ga alamomi da zaku lura dasu da kyau a cikin sati ko sati biyu idan kuna ƙoƙarin yin juna biyu

Ciwon Safiya

Ciwon safe sananne ne ga ko wace mace mai ciki, zata iya faɗa muku, hakan yana iya faruwa ga duk wata mace kuma a kowane lokaci. Wannan itace alama ta farko kafin lokacinku na al'ada ya iso gareku . Lokaci kaɗan idan ciki ya shiga zaku fara jin jiri ko kuma amai da zarar kun fara jin haka wannan itace alama ta farko. Wanda a lokacin jikin ku yana samar da estrogen da progesterone, wasu sinadarai ne, wanda shine sanadin dake haifar da jiri ko amai kamar yadda kwararrun likitoci sukayi bayani ita wannan cutar safiya bata lafawa har sai bayan watanni uku, wannan ciwon safiyar na kamuwa da duk mace yayin da take ɗauke da ciki kafin zuwan al'ada. A riƙe wannan! 

Gajiya 

Wani lokaci dukkanmu muna jin ɗan gajiya da ruɗani a duk lokacin da mukayi aiki ko kuma doguwar tafiya. To Amma ita gajiyar mai ɗauke da juna biyu ya zama dole ta fara samun hakan wanda shike nuna alamomin juna biyu dake tare da ita. Ɗaya daga cikin alamun farkon samun ciki shine tsananin gajiya ko gajiyarwa. Zaku ɗinga samun gajiya ta ayyukan da basu taɓa gajiyar daku ba ada, amma suna iya gajiyar daku a yanzu, kuma hakan na iya saku yin barci da yawa ko da kuwa kun sami sa'o'i 7-9 kuna bacci. Dalili shine, a wannan lokaci jiki yana samar da ƙarin jini don tallafawa jariri mai tasowa, wanda zai iya haifar da gajiya da ƙara muku buƙatar abubuwan gina jiki. Suma waɗannan alamomin samun gajiya suna wucewa a farkon watanni uku kuma hanyar warakarsu shine hanyar hutawa, cin abinci wadataccen abinci mai gina jiki, da shan ruwa mai yawa. 

Canjin nono 

Wannan canjin nono shima alama ce ta farko da yakamata ku mata kusani idan kuna ɗauke da ciki kafin zuwan al'adarku ta kowane wata, wanda tana kasancewa ne a makonnin farko na ciki, zaki rinƙa ganin ƙirjinki na iya zama mai nauyi, mai taushi, kumbura, ko taushi. Wasu mata suna fuskantar wannan alamar kafin lokacinsu na al'ada, don haka ba'a iya ganeta da alamar zuwan al'ada saboda kamanninsu iri ɗaya ne. Koyaya, abu ɗaya dake faruwa a makonnin farko na ciki wanda baya faruwa yayin al'ada, to na al'ada na iya baku labari. Kuma bayan haka kuna iya ganin kan bakin nonuwanku watau nipples ɗinku, na iya yin duhu kuma su ƙara girma.

Spotting (saukan tabon jini) 

Shi wannan spotting yana faruwa ne ga wasu mata za suna ganin saukan tabon jini ɗan kaɗan daga jikinsu wanda hakan shima na ɗaya daga cikin alamomin farko na ɗauke da ciki. Kamar yadda kwararrun likitoci na fannin ciki (juna biyu) suka yi bayanin cewa yayin da kwai ya haɗu da abin dake cikin mahaifa, wannan zai iya haifar da damuwa da zubar jini mara nauyi ga macen da take ɗauke da ciki. Wasu lokutan kuma wannan kan kuskure ne a lissafin lokaci, amma tabo yakan zama mafi sauƙi fiye da lokacin yau da kullun.

Ciwon cikin wata, wannan itama alama ce ta farkon ciki da za'a iya gani amma tana rikicewa wajen banbanta ta da zuwan ala'ada ko lokacin al'ada ita ce take takurawa sosai. Ita wannan lokacin ɗaukar ciki, zaku ga gudan jini yana ƙaruwa. 

Mata da yawa suna fuskantar irin wannan matsalar tun kafin lokacin al'adarsu, amma alama ce ta farkon samun ciki. Don haka, idan kuna da maƙarƙashiya (ko tabo da aka ambata a sama), kada ku daina tunanin cewa kuna da ciki tukuna. 

Canje-canjen abinci

A cikin sha'anin abinci wanda shima hakan yana ɗaya daga cikin alamomin cewa kina ɗauke da ciki. Ita wannan baƙuwar sha'awar abincin ta kayan abinci ce wanda wasu kwararrun likitoci sun aiyana cewa wasu mata zasu ɗinga zaɓan abinci idan zasu ci koyaya, wannan tsattsauran ra'ayin ya samo asali ne daga yawancin mata masu ɗauke da juna biyu (ciki) suna haɓaka sha'awa ko ƙyamar abinci na ƴan makonni bayan ɗaukar ciki. Kina iya samun kanki da sha'awar cin abubuwan daba kasafai kike ci ba ada kafin shigar cikin nan. Abincin da kika fi so kuci ada, yanzu kwatsam za kiji ba kya sha' awarsa. Ko kuma zaka iya rasa ci gaba daya kiji kina kyamar cin abinci wato rashin appetite. 

Jin ƙamshi 

Ga wasu matan dake ɗaukar ciki yana sa su jin ƙamshin su ya wuce gona da iri. Hakan yakansa su suna banbanta yanayin jin ƙamshi tare da su. Misali anan shine sai kiga turaren da bashi da ƙarfi sosai ga sauran mutane na iya zama mai ƙarfi kuma mara daɗi ga matar dake ɗauke da ciki. 

Yawaitar yin fitsari

Wannan yana faruwa ne ba wai shine idan abin dake tare da ke zai ɗinga matse mafitsara a cikin watanni uku ba shine kawai abin dake haifar da yawan fitsari a lokacin ɗaukar ciki ba, wannan ba haka bane. Shi yawan fitsari bayan ɗaukar ciki, yana nufi tare da  nunin cewa ƙodojin mai juna biyu sun fara aiki tuƙuru don tace ƙaruwar gudan jini, wanda ke haifar da sha'awar yin fitsari akai-akai. Wannan alamar zata iya farawa a satin farko na shigar ciki. 

Ciwon kai

A farko shima wannan yana ɗaya daga cikin alamar ɗaukar ciki. Makonnin farko na ciki, zaki iya jin jiri ko kuma ciwon kai mara tsanani a wasu lokuta. Bayan kun yi ciki, jijiyoyin jini ke kumbura don shirya ƙaruwar gudan jini, wanda hakan ke saukar da hawan jini da haifar da wannan jin sauƙin ciwon kan.

Kar a manta da yawa daga cikin alamomin yadda za'a gane shigar ciki a satin farko alamomi ne da ba kowace mace ke gani ba, saboda haka idan ma anji wasu daga cikin alamomin lallai yana da kyau a garzaya asibiti. 

End Alamomin shigar ciki a satin farko na aure.