Gyaran Nono A Sati Daya

Gyaran Nono A Sati Daya

Gyaran nono a sati daya 

Anyi mana tambayane kai tsaye ta hanyoyin da za'a bi domin yin gyaran nono a sati daya, cikin sauƙi, bayanin yadda ƴanmata ko mace budurwa zata gyara nonuwanta. Wayyo!.. Ai dama wannan aikin at some point, akan gaɓa kenan akwai buƙatar namiji ya yiwa mace cikakken bayani akan yadda zata gyara masa nonuwanta, mace budurwa zalla fa kai har ma da matan aure, domin matan aure zae fi amfanarku! kuji ni da kyau yauwa to!..

Na kuwa amshi wannan aikin da hannu bibbiyu ba domin komai ba, sai ko domin ku ƴanmata zaku fi ganewa, ku kuma fi fahimtar yadda nonuwanku suke tsone idanun namiji musamman ma idan shi wannan namijin yasan ku ƴanmata ne, ko kuma ke ɗin budurwa ce ma'ana dai idan yasan baki da aure.

Gyaran nono
Gyaran nono post pic#

Idan namiji yasan haka to nonuwanki sunfi tsone masa ido tunda ai yasan babu mamallakin nonon, idan kina da albarkatun ƙirji ko kuma kina da kyawun nono, ko kuma nonuwanki masu ɗaukar hankali ne irin wanda zasu sa namiji jin ina ma ya mallake su, namiji ya riƙa jin daɗin kalle miki na shanun ki, yaji yana mafarkin taɓa su da yin wasa dasu ko kuma ya riƙa burin cika hannunsa da manyan nonuwanki, ko ya riƙa tunanin ina ma ya samu ya sha su ya ƙoshi. 

Koma dai wanne ne a ciki to ke ƴanmata kin kwan da sanin kula da baiwar ƙirjinki wajibi ne. Na lissafo duk abubuwan dana lissafo a baya ne saboda nasan kuma ƴanmata kunsan nonuwanku suna tsonewa mazaje ido don koni ɗinnan fa sai a hankali, domin ni fan ɗin matasan nonon budurwa ne ƴar shila lamba ɗaya. Babu ƙarya nonon budurwa matashiya baiwa ne, kuma abin so ne, abin burgewa. 

Bari dai karna cika ku da surutu duk da dai akwai magana a bakina sosai amma haka zan yanke saboda mu tsunduma cikin bayanin yadda ke budurwa ko yanmata zaku gyara nonuwanku. 

Babban jan hankali anan shine; idan ku ƴanmata ne ko kuma ke budurwace, ina nufin ke mai karanta wannan bayanin, ki sani cewa shan kwayoyin bature ko kuma wasu magungunan domin ƙara miki cika da girman nono, to kibi sannu a hankali, kar kiyi garaje domin hausawa suna cewa 'garin neman gira akan rasa ido kuma a wata faɗar suka sake cewa zafin nema baya kawo samu. To kamar hakane akanki ƴanmata ko ƴar budurwa. 

Ire irenku masu ganin cewa ƙirjinku bashi da girma bari kusha wani abun da zai sa ƙirjinku ya cika, kuna nan da yawa na sani, amma duk ku dakata ku bani hankulanku, kuji ni da kyau;  halittarku ta mata tana gama cika ne a dakunan mazajen ku, saboda haka idan kuka bi a sannu ko baku sha komai ba, zaku samo wannan girman nonon ne da kuma cikarsa ne a hannun mazajenku bayan kun shiga dakunan ku. 

Idan kika je kina shan magunguna na ƙarin cikar nonuwanki ranar duk da nonuwanki suka cigaba da girma saboda taɓawar da mijinki yake musu, tofa saurin zubewa zasuyi. Wannan shine matsalar don haka ku gane kuma ku kiyaye. 

Ki sani a wasanni da duk abinda miji zaiyi da ƙirjinki, ko da baki ɗauki cikinsa ba dole zaki ga chanji a nonuwanki saboda zasu riƙa cika suna ƙara girma bayan wani lokaci idan yana taɓa su. Saboda haka yake budurwa, kifi maida hankali akan lafiya da kuma gyaran nonuwanki ba ƙarin girmansu ba yayin da kike budurwa. 

Akwai mata ƙalilan waɗanda ba lallai nonuwansu suyi girma ba koda sun haɗu da namiji, irin matan nan sune suke da buƙatar yin amfani da magunguna domin neman cikar ƙirji, suma kuma ɗin sai bayan sunyi auren ne zasu gane hakan. 

Tare da haka kuma har ila yau akwai wani abun lura daya rage mana guda ɗaya wanda za'ayi magana akansa kafin a fara bayanin hanyoyin gyaran nono. Abin lura anan kuwa shine ba'a so mace ta riƙa saka riga ko bra wacce ta matseta sosai saboda haka zai riƙa danne glands ɗin nonuwa, kuma daga waɗannan glands ɗin sunyi weak to dole nono zai faɗi. Yana kuma saka jijiyoyin jikin nono suyi sanyi su saki, a irin hakane nono yake zubewa. Domin haka yaku ƴanmata ko budurwar dake tare dani anan, ku riƙa sanya bra wacce take da faɗin hannu da baya saboda tafi balance kuma tafi support. 

Hanyoyin gyaran nono ga budurwa.

_____________________________________

Hanyar gyaran nono ta farko:

Waken suya

Riɗi 

Aya 

A samu waken suya a gyara shi a cire dattin cikinsa sannan a saka a wuta a soya. Ya zama suyar sama-sama kuma waken suyar kaɗai kar asaka mai, Idan akaji ya fara ƙamshi sai a sauke. Sannan a samu riɗi shima a soya sama sama a sauke, idan duka soyayyun waken suya da riɗin nan suka bushe sai a daka su. Kullum da safe sai a ɗiba, wannan dakakken waken suyar a zuba a ruwan zafi a sha, sannan a samu kunun aya mai kyau a zuba garin riɗin nan shima asha sau uku a rana. 

Wancan na waken suya sau ɗaya za'a sha da safe kafin aci komai, na riɗi da kunun aya kuma sau uku, sannan a riƙa shafa man riɗin akan mama.

Wannan watau wani haɗi ne na bayyana muku shi yanzun nan, kuma shi ɗin na musamman ne, domin duk abubuwan da aka lissafa muku tun daga; waken suya, riɗi, aya dashi kansa man riɗin sune abincin nono. Saboda haka za kiga yadda nonuwanki zasu ciko su riƙa cika ƙirjinki da rigarki taf kamar yadda kike so kuma ba tare da kinsha wani maganin bature ko wani wanda zaiyi miki illa a gaba ba. Haka kuma jikinki zaiyi kyau sannan kuma ga ni'ima nasha-nasha. 

__________________________________

Hanyar gyaran nono ta biyu:

Lalle na gargajiya 

Bagaruwa ta hausa

Garin habbatus sauda

Garin hulba 

A ɗebi kowanne cikin babban cokali sannan a zuba ruwa iya yadda zai isheki ki zauna a cikin sa. Sai ki dafa ruwan sannan ki bari yasha iska yadda zaki iya zama a ciki, sai ki tace shi a baho sannan ki shiga ciki ki zauna ya shiga jikin ki sosai, bayan kuma kin fito daga tsumuwar nan da kikayi sai ki samo man tafarnuwa ki haɗa da farin miski, kisa auduga a ciki sai ki cire kiyi tsome in ya kai tsahon awa ɗaya sai ki cire. Kiyi wannan kwana biyar jere da juna babu fashi. Idan kika jure kikayi babu fashi to la budda babu makawa zaki bawa wasu labarin irin nasarorin da kika samu. 

__________________________________

Hanyar gyaran nono ta uku:

Ki samu kankana guda ɗaya, kwakwa guda ɗaya da dabino kofi ɗaya, sai ki yanka kankana da wannan gwandar gaba ɗayansu ki zuba su a guri ɗaya, daga nana sai ki cire duk kwallayen dabinon nan ki wankesu suma ki zuba, sai ki samu wani abu mai ƙarfi kamar ludayin ƙarfe kiyi ta juyasu har sai kankanar nan ta zama ruwa, sai a rufe a saka a cikin fridge ya kwana. Idan ya kwana da safe sai a ɗauko a saka madarar ruwa gwangwani ɗaya da zuma daidai yadda ake so, daga nan kuma sai ayi blending yayi laushi. Idan yayi kauri za'a iya ƙara ruwa, sai a wuni ana shansa. 

Wannan haɗin yana saukar da ruwa a nono sannan ya ciki taf ya kuma tsaya a tsaye gwanin sha'awa. Abi duk bayanin da akayi a sama ayi su daki daki, za'aga abun mamaki.

_____________________________________

Hanyar gyaran nono ta hudu:

Dabino 

Madarar shanu 

Kaninfari (gari) 

Kirfa 

Za'a fara shanya dabino ya bushe sai a cire kwallon a daka shi ya daku sai a haɗeshi da garin kaninfari da kuma kirfa a cakwuɗa su, sai a riƙa zuba cokali uku ana haɗawa da madarar shanu, ana sha safe da yamma cokali uku uku kullum tsahon mako ɗaya. 

Wannan haɗin zaisa su ciko idan sun yamushe. Zasu tsaya su cika suyi ɓul ɓul ko ina taf taf, ya gyaru yayi kyau da inganci. 

Da wannan na kawo ƙarshen yadda ƴanmata ko budurwa zata gyara nonuwanta. A karanta a nutse, sannan a jarraba domin samun cikakken sakamako.

Na barku lapia!

End of gyaran nono cikin sauƙi post#

Post a Comment

0 Comments