Yadda amarya zatayi a daren farko post#
Amarya bakya laifi ko kin kashe É—an masu gida! Ku faÉ—amin wanene yafi Amarya farin jini ? Sai dai idan ba amaryar take ba. Amma indai sunanki amarya, kuma amaryarsa, amaryar gaske, to a wannan ranar taki ba yake. Baki da tsara!
Ina wannan amaryar da take da burin ko fatan ta mallake angonta a daren farko ?
Ina wannan amaryar da take mafarkin mijinta ya ɗaukota in a bridal style. Ma'ana irin yadda ango yake ɗaukan amaryarsa cikin shauƙi, lallami kuma cike da soyayya bayan sun raya darensu na farko kuma ya rayu ?
Idan kina cikin irin amaren nan to ina miki albishir. Goro fari ƙal! Wannan rubutun naki ne. Kizo ki karanta shi ki gane, sannan kiyi tafiyarki. Zaki dawo ki godemin daga baya, banda gaggawa ina nan.
Amarsu ta Ango! Alƙalamina kacokan yau akanki yake, ki matso ki bani hankalinki saboda ina mai tabbatar miki cewar idan kika biyoni a sannu, kika fahimci wannan blue print ɗin ko nace taswira ta yadda ya kamata kiyi a darenki na farko tare da ango, to zaki sameshi a tafin hannunki daga wannan daren har zuwa darenku na ƙarshe tare, dan nasan hakan kika fiso, kuma haka kike fata.
Idan kuwa hakan ne to kisani, aikinki zai fara ne a wannan daren, nasan kin sani sarai, amma ki sani, amare da yawa sukan aro wani tunani su ɗorawa kansu ayayin da wannan daren yake kusanto su, kuma wannan tunanin ya tasirantu a cikin zuciyoyinsu da kwakwalwarsu, wanda a dalilin hakan wannan daren nasu na farko tare da ango, a maimakon su bugashi a matsayin final, ma'ana dai wasan cin kofi sai kiga sun bar wannan damar ta suɓuce.
Idan kika bari wannan damar ta suɓuce miki kuwa to ki sani yake Amarya, jan aikin dake gabanki na mallakar angonki ya nunku sau ba adadi. Baza ki gane hakan ba har sai kin fahimci irin ta'asar da kika yiwa angon naki, wanda ya daɗe da cin burin wannan daren farkon naku.
Yawa yawan tunanin da amaren nan ke arowa su azawa kansu, tunani ne da yake yaudarar hankalinsu. Idan amarya ta shiga zulumin abubuwan da zasu faru a daren farkonta, tunaninta a wuri É—aya yake curewa shiyasa dabara take toshe musu a wannan É—an rintsin. Tabbas kiji ni da kyau, haka yake. Kina cikin rintsi amma na É—an lokaci.
Zulumi shine abinda yafi damun yawancin irin amaren nan. Zulumi da tunane tunane kamar haka;
*Ance fa akwai zafi sosai*
*Ta yaya zan kuɓucewa wannan zafi ko raɗaɗin*
*Kina tsoron ango ya afko miki*
*Kina jin kunyar hangoku ke da ango a wannan yanayin*
Irin misalan zulumi ko tsoro da fargaba da amarya zata riƙaji kenan, amma amarya tasani wannan duk normal ne. Koda ace amarya ta karanta wannan rubutun, ta kuma fahimceshi ma'ana dai ta shirya tarɓar angonta, still, ayayin da akazo kan gaɓa zaiyi wuya bataji zulumin nan ko tsoro ya ɗarsu a ranta ba.
Yake Amarya ki ɗauki darenki na farko a matsayin ƙurar data taso mai ƙarfi amma fa zata lafa bayan ɗan lokaci, indai ba rashin sa'a ba. Ita kuwa rashin sa'a dama ana sakata a lissafi, mai lissafine yasan haka.
Saboda haka idan kina da lissafi yake amarya, a yayin da daren farkonki yake fuskanto ki tare da angonki, shawarar farko dazan baki, kijini da kunnuwanki biyu;
"Karki riƙa lissafin abinda ya faru da wasu ƙawayenki ko wasu ƴan uwanki anasu daren farkon tare da nasu angwayen. Su, sune su. Ke kuma yau kike amaryarsa. Naki labarin daban ne da nasu. Ƙaddarar daren farkonki takice ke kaɗai kamar yadda na kowace amarya yake daban.
Angonki ba angonsu bane. Kai a taƙaice ma wai ina lissafin naki yake?
Ki tuno cewa ko alhaji mai mata uku kika aura ya cikeki ata huÉ—un su, a wannan daren ke kaÉ—aice amaryarsa a duniya. Uwargida da ragowar matansa biyu shi É—in miji ne a garesu, ke kuwa angonki ne. Kin fahimci irin alfarmar da kike da ita kuwa yake amarya?
To kuwa idan kina da irin wannan alfarmar me zaisa ki damu da labarin ƙawayenki da nasu mazan?
Cikin kaso É—ari na yadda za'a ja ragamar daren farko, kusan kashi tamanin zuwa casa'in na ango ne. Idan ke amarya ce mai wayo wacce tasan abinda takeyi, kisa angonki yabi yadda kike so wurin jan ragamar daya samu.
"If you can't make him think as you do, make him do as you think..
Ita kaÉ—aice shawarar dazan iya baki amarya, abin da kawai ya rage sai dai na biki da fatan alheri. Dalili kuwa shine idan har baki É—aura niyyar bin shawarata dana ambata a sama ba, to duk wasu hanyoyin da wannan rubutun zai nuna miki, bazaki É—au haske akansu ba, ballantana ma ki karanta ki kuma fahimta har suyi miki amfani. Hakan kamar da wuya.
Dole ne sai kin fuskanci reality kafin daren farkonki yayi kyau yayi armashi tare da ango.
Idan amarya ta karɓi shawarar dana bata, to ki biyoni a ƙasa inda zan bayyana miki makaman yaƙinki na daren farko kamar haka;
-Gyaran jiki
-Shagwaɓa
-Yanga
-Ƙamshi
-Kunya
Gyaran jiki-
Gyaran jikinki wani makamine wanda zaki fara tanada watanni ko satittika kafin daren farkonki, ko nace daren yaƙin soyayyarki. Kuma dashi wannan makamin naki ɗaya tal zaki iya cin galabar wannan yaƙin a ƙarshe.
Nasani amma nasan ku jinsin mata kun fini sanin abubuwan da kuke amfani dasu wurin gyaran jikin amare. Kuma nasan har akwai matan ma da ake hayowa ko kuma a ɗauki amarya kacokan akai musu ita dansu gyarata su fimfawa ango ita. Ko ƙaryane ?
Haka kuma na sani sarai iyayen amarya da ƴan uwa wato dangi, ƙawayen amarya, kai a wasu lokutan ma har ita amaryar kanta duk suna kashe dubban nairori wurin gyaran jikin amarya kafin biki, saboda idan bikin yazo sai dai kuma a sake sabon lale domin kuwa cacar kuɗin zata tashine daga kan masu gyaran jikin amarya ta koma kan masu yi mata make up, watau kwalliyar fitar biki ita da muƙarrabanta.
Duk amarya Æ´ar gata ana mata wannan. Masu rangwamen gatan ma suna samun dai dai nasu. Saboda abin naku iya kuÉ—inka iya shagalinka ne!
A cikin irin ababen da kuke amfani dasu nasan akwai su kur kur da alawa domin gyaran fata, dasu dangin humra domin ƙamshi, koma dai da menene za'a tsumawa ango ke amarya, dole ki gyara jikinki domin ƙarowa kanki ni'ima idan kina da ita, ko kuma nemo ni'imar idan kin kasance baki da ita.
Idan kana da kyau akace ka ƙara da wanka..
Shagwaɓa-
Ki zuba masa shagwaa son ranki a wannan daren domin ke din yar lallami ce. Shagwabace makamin da yafi yawa a cikin makaman yakinki, fahimtar hakan shi zaisa kisan muhimmancinta ko amfaninta a wurinki.
Idan mace ta shagala wurin zubawa mijinta shagwaɓa to ba daren farko ba inma akwai daren ƙarshe to ina mai tabbatar miki kina ransa komai tsufanku.
Wane ɗan auta ko ƴar auta ? Babu wanda yake da dalilin yin shagwaɓa, ya kuma cancanci yayi shagwaɓa yadda yake so kamar amarya a daren farko. Idan amarya ta gane wannan karatun to tamkar taci wasan daza a buga ne a daren farkon, abinda ya rage kawai shine aikatawa.
Ki masa shagwaɓa amarya, wannan ce babbar damarki na amfani da tambarin naki na amaryarsa, kisa aranki angonki na nan yana jira yana kuma mararin shagwaɓarki.
Yanga-
ÆŠazu a sama ba kiji nace ke Æ´ar lallami bace ? Amarya ai dole sai da lallami a wurin ango. Kiyi yanga yadda kikeso amma fa yanga ta lissafi, yanga abin burgewa ga angon naki.
Yanga a salo na tafiya, karya harshe da murya, lafazi mai daÉ—i a cikin salo na magana, murmushi mai kyau da É—aukar hankali, dariya mai daÉ—i da tsari..
Kamar yadda koyaushe nake tunatar da mace, jan aji wani jigo ne a rayuwarki, to kisan yacce zakiyi jan ajinki yazo a wannan daren amma fa a sifa ta yanga !
Ƙamshi-
Baki amarya idan har bakya ƙamshi! Me kikeyi da har bakya ƙamshi kuma kina amsa sunan amarya? Lallai da sake!
Ƙamshi da kike gani shine katinki na ƙarshe a wasan kati na caca wanda dashine zakiyi abinda ake kira check !
A turance !..
Ƙamshin dake tashi a jikinki shi zai janyo miki kusancin ango ba tare daya shirya ba tamkar mayen ƙarfe.
Amarya, ƙamshi bana kayan jikinki ba, ƙamshin dake tashi a fatarki. Karki manta dama saida na faɗa miki a sama, gyaran jiki shine makaminki daya tal na cin yaƙin daren farkonki. Zaki samo ƙamshin da ake nufine a wurin gyaran jikin nan.
Ƙamshinki shi zai sururuta angonki a wannan daren zuwa gareki, idan kika riƙi ƙamshi daga sannan kuma, to ki tsumayi angon naki kusan koda yaushe cikin son samun kusanci dake, wanda haka kuma ko ban fito na faɗa miki ba, kema kinsan nasarace a wurinki.
Kunya-
Yake amarya bana zaton kina da wani makami da yake buƙatar saiti kafin kiyi amfani dashi kamar kunya ba. Kunya makaminki ce wacce idan kika samu kika daidaita ta, wane ango ko sarkine angon naki, to kin haye a wurinsa.
Karki yadda kunyarki ta gaza, ma'ana tayi ƙaranci har yaga rawar kanki haka zalika karki yadda kunyarki tayi yawa wurin kusancinku dashi har a samu tangarɗa wurin raya daren, idan haka ta faru to kin gaza a idon ango.
Idan kika daidaita kunyarki, kika yita a inda ya dace kiyi ta, kika kuma barta a lokacin daya dace, to la budda; inji larabawa watau babu makawa kenan inji bahaushe, bature kuma yace inevitable! To haka cin jarabawar daren farko zata zo miki.
Kiyi nazari akan makaman dana lissafo miki, na kuma yi miki bayaninsu, na yadda ya kamata ki sarrafasu a darenki na farko tare da ango. Na barki lafiya..
Yadda amarya zatayi a daren farko post#