Yadda ake sa budurwa dariya post

Barka da zuwa wannan shafi namu na kayan marmari gamida soyayya ta more rayuwa, a yau idan mai duka ya nufa za muyi magana ne akan yadda ake sa budurwa dariya. 

Hanyoyin da ake sa mace dariya ko kuma nace nishaÉ—i suna da dama sosai. Amma za muyi magana akan wasu daga cikin hanyoyin.

Saka budurwarka dariya abu ne ma sauki saboda ina tabbatar maka da cewa bashi da wahala musamman idan ya kasance tana sonka sosai. Kai idan budurwa tana sonka, to cikin sauÆ™i zaka fahimci cewa abu kaÉ—an zaka yi mata kaganta ta soma dariya. Maganar gaskiya wasu lokutan ma abun bana dariya bane amma zaka ga tana dariya, inayi maka murna domin da zarar kaga an kai wannan mataki, tofa a gaskiya budurwarka tana yinka yadda ya kamata 

A cikin hirar soyayya na yadda ake sa mace dariya abu ne me sauƙi amma fa ga wanda ya fahimci halayen budurwarsa kuma yasan abubuwan dake faranta mata rai da akasin hakan. Abun nufi anan shine idan ka gane abubuwan dake saka ta cikin farinciki to saika yawaita ambatar wadannan abubuwa da take so, harma da kuma yabonta ko zugata, saboda yaba halayen mace da kyawunta da dai sauransu suna sanyata dariya da murmushi ba tareda ta shirya ba wanda a ƙarshe sai ta kwana cikin farinciki wanda hakan shine burinka.

Yadda ake sa budurwa dariya
Yadda ake sa budurwa dariya post

Kuma yan daga cikin yadda ake sa budurwa dariya yawan yi mata wasanni misali nace, barkwanci da ƙaƙalo labaran ban dariya kai a wasu lokutan ma har dana shirme amma wanda a cikinsu ba cin fuska ko kuma rainin hankali ko wani abu makamancin haka, to ina tabbatar maka da cewa hakan zai saka budurwarka dariya sosai.

Ko ba'a faÉ—a ba wannan a zaune take cewa duk masoyi ko kuma saurayi me yawan surutu idan yana hira da budurwarsa baya shan wahala wajen saka budurwarsa dariya. Musamman ma idan yana maida hankali wajen kula da abinda ke sata dariyar kuma yana yawaita su. 

Amma idan ya kasance saurayi bashi da yawan magana to ga abinda ya kamata ya dunga yi mata:

Mata da yawa na son yabo. Saika dage wajen yabon babynka da kyawunta, yaba halayenta masu kyau waɗanda yasa kake alfahari da ita. Sannan ka rinƙa bata labarin irin rayuwar da kake fata ku gina kai da ita a cikin rayuwarku ta aure. Abu mai muhimmanci ka gaya mata irin soyayyar da kake yi mata wacce baza ta misaltu ba. Da irin bata labarin wani abu daya faru da bata san anyi ba cikin salo na barkwanci.

Misali: idan sunan budurwarka Fatima.

Idan kaje zance gunta tana fitowa izuwa gareka, saika saki fuska cikin murmushi da annuri kace hmm wai dama kece kika fito aini naga wata kyakkyawar zankaÉ—eÉ—iyar budurwa ta nufo ni kwata-kwata bangane ke bace, ba kiga ina waige-waige ba ?

Yaufa cikin sauƙi zaka samu kyautar murmushi mai tarwatsa zuciya tareda ƙarin ƙaunarka da soyayyarka cikin zuciyarta.

Bayan kun gaisa kaji yaya lafiyar babynka saika É—an soma bata wasu zafafan kalaman soyayya, bayan kaÉ—an kumbura mata kai da kalamai sannan saika soma haÉ—awa da wasu labaran nishadi masu fasa ciki wajen dariya.

Anan muka kawo ƙarshen wannan rubutu namu, amma a cikin rufewa bari mu gaya maka abubuwa na yadda ake sa budurwa dariya sune kamar haka:

1. Sakin fuska

2. Murmushi

3. Ƙaƙalo dariya

4. Labaran barkwanci

Da dai sauransu.