Yadda ake jan hankalin saurayi complete article#

Abubuwan da yan-mata ya kamata suyi domin jan hankalin saurayi.

Mata adon gari !

Mata iyayen nishaɗi !

Mata birnin ni'ima !

Kamar yadda kowa ya sani mu a matsayin-mu na samari mata abin son mune! haka suma ta bangaren yan'matan.

In ma dai saurayinki ne ko kuma yana birgeki kina son ki janyo hankalinsa gareki kina da hanyoyin daza kiyi amfani dasu wajen cimma burinki. Ƴan mata kiyarda cewar namiji yasan lagonsa, yasan hanyoyi da yawa wanda idan aka bi dashi zai faɗa tarkonki, saboda hausawa masu iya magana suna cewa "mai ɗaki shiya san inda yake masa yoyo". Kuma hakan take. Sai dai kuma hausawan dai masu iya magana, a wata faɗar tasu kuma suna cewa; "idan yasan wata, bai san wata ba". Wannan zancen nasu ma babu ƙarya haka yake domin kuwa ba komai da komai mutum zai iya sani ba. 

A cikin hanyoyin da zaki bi ki janyo hankalin saurayi a wannan rubutun da zaki karanta, wasu ya sansu, haka zalika akwai waɗanda tabbas zaki shammaceshi dasu ya faɗa komarki ko tarkonki da kike ɗana masa domin kuwa bai sansu ba shiyasa bai kuma yi tsammaninsu ba. 

Yadda ake jan hankalin saurayi
Yadda ake jan hankalin saurayi article#

A cikin hanyoyin da zamuyi bayani, kowanne yana ɗauke da sifa ɗaya wacce zaki ɗauka ki faɗaɗa ta kiyi kuma aiki da ita, a matsayinki na mai neman cikar wani buri, burinki na janyo hankalinsa kuma burinki na samun soyayyarsa. Shi wannan saurayin. 

Siffofin sune kamar haka;

-Ado da kwalliya

-Iya magana 

-Tafiya 

-Jan aji

-Ƙissa

-Kulawa 

:. Ga bayanin siffofin yadda ake jan hankalin saurayi daki daki.

-Ado da kwalliya

Mata adon gari. Karki yadda ki manta da wannan kirarin naku, kowa yasan mace ƴar ado ce. A taƙaice kafin muyi dogon bayani a cikin wannan sifar, Kiyi wani tunani guda ɗaya, idan har so kike ki janyo hankalinsa zuwa gareki, Ai dole akwai buƙatar ya kalleki ko ? Sai ya fara kallonki kafin fa hankalinsa ya kai zuwa gare ki. 

Idan kin gane haka to tabbas kin fahimci ado da kwalliya yanzu sun wajaba a kanki, kin kuma fahimci cewar ado da kwalliyar nan farillai ne su akanki a wannan tafarkin na cikar burinki, wanda shine jan hankalinsa. 

Fahimtar hakan wata alama ce ta nasara amma baza kikai ga cimmata ba, har sai idan kin aiwatar da ita. 

Karki yadda kice ko kiyi tunanin zanja hankalinsa da kyan siffata, kyan fuskata, kyan diri na. A'a sam ƴanmata, karki yadda kibar wannan tunanin yayi tasiri a cikin zuciyarki, tasirinsa giɓi ne ga cikar burinki. Ai abinda ya kamata ki tuna shine maganar nan dai ta hausawa da suke cewa "idan kana da kyau, ka ƙara da wanka". A domin haka kiyi wanka, ado da kwalliya ƴan mata. 

Kin yarda kina buƙatar ado da kwalliya domin kija hankalinsa, mai ya rage miki ? Yinta. Amma fa sai kinyi ta dai dai. Dai dai da yadda zaki burge shi. Ba kowace kwalliya ce zata burgeshi ba, kisa wannan a ranki tun wuri.

Ki riƙa yin kwalliya saisa saisa musamman idan kinsan akwai yiwuwar ku haɗu ko kuma kinsan zai iya ganinki; ma'ana kwalliya mai kyau da tsari amma sama sama karki riƙa yi masa kwalliya kamar mai zuwa party ko gidan biki ko kiyi kwalliya kamar ta hannun damar amarya koma amaryar da kanta. A'a. Idan kikai haƙuri kika bi asannu sai kiga wannan lokacin yazo. Har ila yau karki manta, hausawa masu iya magana suna cewa "mai haƙuri yakan dafa dutse harma yasha romonsa ya gyatse. Tabbas! Haka ƙarfin haƙuri yake. 

Yawa yawan maza kwalliyar da akayi ta a sauƙaƙe wacce kika fi saninta da suna "light make up", tafi burgesu. Idan harke ɗin kina cikin rukunin mata da ake kiransu ƴanmata ba matan aure ba, to ki lazumci yinta akan idon saurayi, zaki fi samun chance, watau dama tajan hankalinsa fiye da kwalliyar da kuke yiwa laƙabi da "heavy make up", a turance inji masu jajayen kunnuwa. 

Wannan kwalliyar ta heavy make up tafi buƙatuwa da cancanta a wurin amarya da ƙawayenta, ko uwargida sarautar mata, da duk macen da idan tayi irin wannan kwalliyar to tasan dan wa tayi. Shiyasa nakeso ki gane cewa idan kikaje kina masa kwalliyar heavy make up "to lallai zai fahimci kin damu dashi. Kar kiso hakan, ba alamun nasara bane. A can gaba zan faɗa miki dalili. Ki biyoni a sannu. 

Kwalliyarki ta light make up ya zamana musamman ta haɗa da gyaran gashinki, fuskarki ta zamana fes fes, haka laɓɓanki, kisan irin jan baki ko lip sticks din daya dace dake, duka dai. 

Menene kuma ado ? Kwalliyarki itace cikamakin adonki. Duk abinda zaki sanya a jikinki wanda yake a fili, wanda za'a gani, ba under wear ba sunansa ado. A gashinki akwai abin ado kamar ribbon, a wuyanki akwai sarƙa, rigar jikinki, zoben hannunki da duk sauran misalan daban ambata ba. 

______________________________

-Iya magana 

Magana dai munsan jari ce. Idan kinso, zaki iya amfani da daɗaɗan lafuzanki, da hikimar iya magana ki riƙa burgeshi dasu, ta wannan hanyar idan baki rainata ba, sai kiga ya shigo hannunki dumu dumu. Ki sani yake ƴanmata, maza da yawa sunso mata, sun kuma auri mata, suna kuma zaune da wasu matan ne ba don komai ba sai don saboda iya maganar su waɗannan matan, da kuma irin daɗaɗan zancensu. 

Maganganunki ko kalamai masu sanyaya rai, masu janyo hankali, masu kwantar da zuciya haka kuma masu samun gurbi su zauna daram a cikin zuciyar, sune fa maganganun ko kalaman da zai riƙa tunawa wataran koda ace ba kya kusa dashi, to ina kuma ga kinayin sune a yanzu da kike ƙoƙarin janyo hankalinsa? Ki auna ki gani zaki fahimci lissafin sosai. 

Wannan siffar ta iya magana ko zance na ɗaya daga cikin irin sifofin da namiji ba lallai ne ya ankara ko yayi tsammaninsu a matsayin kina son karkato da hankalinsa kanki bane, ki gaggauta sasu a cikin lissafinki, ki kuma ɗaura niyyar yin aiki dasu, ina gaya miki zakisha mamaki idan kika ga ya faɗo tarkonki saboda hakan. Sai dai kuma kar kiyi mamakin hakan tunda dama ai an tuna miki;

Magana jari ce! Yaro bada kuɗi a gaya maka. Sai kuma a cikin jarin ne ake iyayin guzuri yayin tafiya. Lallai ki iya kalamai da zance na soyayya.

______________________________

-Iya tafiya 

Kar kiyi mamaki don nace miki tafiyarki zata taimaka ko kuma zata iya janyo miki hankalin saurayi ? Namiji sau tari yakan hango nutsuwar mace a iya yanayin tafiyarta. Kinga idan kikayi takun ki ɗai ɗai, tunma ba'a je ga yin ado da kwalliya ba, ba tare da kinyi magana yaji yanayin lafazinki ba, tafiyarki kaɗai tana neman ta janye akalarsa zuwa gareki. 

Duk wani namiji da kika sani yana son yaga mace a nutse, to kuwa tunda har zai lissafa nutsuwarki a nau'in ko kuma yanayin tafiyarki, kiyi takunki ɗai ɗai, kiyi rausaya kuma kiyi yanga ko yaya take a cikin tafiyarki. Zaki burgeshi. 

_____________________________

-Jan aji

Idan kina tare dani a rubutun nan to ɗazu a baya nace; idan kina yiwa namiji kwalliyar da zai gane don ki burge shine to lallai zai fahimci kin damu dashi. Kar kiso hakan, ba alamun nasara bane. Ga dalili na, shine *jan aji*..

Jan aji watau class, yana cafkowa ko kuma nace waftowa mace maki mai kauri a wurin ɗa namiji. Mace mai aji sunan ta Macen data san kanta, faƙat ! Haka zancen yake. Kin sani, na sani, ya sani kuma kowama yasan wannan. Ki riƙe ajinki shi kuma zai biyoki. 

Mace mai aji na gaske daya amsa sunansa aji, ma'ana yarinya mai class irin ƴan matan nan suna buƙatar ado da kwalliya, iya magana, tafiya amma idan sun gaza ko yaya ne, wannan ajin nasu shi zai taimaka musu a wurin janyo hankalinsa. Ja ajinki da kyau ƴanmata ! 

____________________________

-Ƙissa

Mace mai ƙissa, Mace kenan mai tayarwa da kishiya hankali cikin ruwan sanyi. Mata duka sun san wannan. Mace mai ƙissa tana daga gefe take kallon cikar burikanta da yawa. Mace mai ƙissa ta haɗa komai da komai. 

Ki auna ki gani, ƙissar mace a tsakanin kishiyoyi guda huɗu, uku ko biyu takan kwato ta harma taci yaƙin data ke bugawa dasu waɗannan kishiyoyin nata. To ina kuma gake ƴanmata, gwada taki baiwar ƙissar kiga irin gudunmuwar da zata baki. Zaki ga abin al'ajabi. Ina gaya miki!

Idan ƙissarki tayi dai dai to dole ki janyo hankalinsa kai harma ki ganshi ya shigo hannunki, kuma idan kika riƙeta dai dai sai kiga kin mallakeshi gaba ɗaya. Yadda zaki sarrafa ado da kwalliyarki, iya maganarki, tafiyarki, da jan ajinki duk suna cikin ilimin ƙissa ne. Kinga kuwa dole ne mace ƴar kissa tayiwa ragowar mata zarra a idon namiji. 

____________________________

-Kulawa

Sifar da aka zaɓa tazo a ƙarshe cikin hanyoyin ko kuma abubuwan da ƴanmata zasuyi su janyo hankalin saurayi a cikin wannan rubutun itace kulawa. Tazo ne a ƙarshe ba wai don ragowar hanyoyin da akayi bayani a sama sun fita muhimmanci bane. Sam! Ba haka bane. Kamar yadda masu jajayen kunnuwa suke faɗa ne; da suke cewa "last but not the least"..

Wannan sifar ta kulawa tazo ne a ƙarshe saboda ita ƙarashen tafiyace akan tafarkin da kike tafiya akai na ganin cikar burinki wurin janyo hankalin saurayi. Idan har kinyi waɗancan ayyukan da kyau yadda ya dace to ki ƙarasasu da wannan, kiyi abin nan da bature yake cewa "icing on the cake".. 

Wane mutum ne bai son kulawa ? Kowa yana buƙatar kulawa daga wani nasa. Kuma kowa yana buƙatar yaga wani ya nuna kulawarsa akansa. Maigida yana jin daɗin zama da macen da tafi kula dashi acikin kishiyoyi, irin wannan sifar taki ta nuna masa kulawa yake ɗiya mace, itace zata saki ki shiga ransa. Idan kuwa har kin shiga ransa to hankalinsa yana wajenki, idan kuma hankalinsa yana wajenki ai kuma burinki ya cika ƴanmata ! Domin haka ki nunawa saurayin kulawa cikin salon da dabara..

Yadda ake jan hankalin saurayi post# shafinbatsa.com.ng all rights reserved.