Karin ni'ima cikin sauki article#

Ni'ima abace mai matukar muhimmanci a tattare da mace domin kuwa tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantacciyar mace, wacce ta amsa suna mace mai dadi, idan kinada ni'ima keda kanki kinsan hakan, saboda mata masu wadatacciyar ni'ima sun fita daban, domin kallo É—aya zaka yiwa mace ka tabbatar cewa eh lallai wannan za tayi daÉ—i.

Kamar yadda yan uwa masu ziyartar wannan shafi namu na kayan alatun lambu suka buƙata, a yau za muyi bayani akan za'a haɗa magani wanda yake ƙarawa mace ni'ima kuma wannan haɗi yana kara lafiyar jiki yadda ya kamata ga ma'aurata bama ta ƙarin ni'ima kaɗai ba.

Karin ni'ima cikin sauki
Karin ni'ima cikin sauki post

Abubuwan da za'a nema domin karin ni'ima cikin sauki, sun haÉ—a da.

1. Dabino mai kyau

2. Girfa (Cinnamon)

3. Busasshiyar citta

4. Zuma mai kyau.

1. Dabino za'a samo mai kyau irin ɗan Nijar haka, wanda ya bushe sosai, wanda bazai dinga danƙarewa lokacin niƙa ko blending ba, zaki ɓarashi ki cire duk wasu kwallaye dake cikinsa sannan ki mayar cikin ɗan bokitinki.

2. Girfa a samu cinnamon me kyau kuma isasshiya.

3. Citta a samo Itama wacce tasha rana ta bushe, ta yanda za'a gane ta bushe kuwa shine a karya da hannu idan É—aya ce to bazata karyu ba.

4. Zuma gyararriya kuma tatacciya mai kyau sosai, domin zumar kala kala ce kar ayi amfani da baƙa ko wani samfuri da babu shi a zuma, daidaitacciyar zuma itace me ruwan garai a kalarta.

Yadda za'a haÉ—a haÉ—in karin ni'ima cikin sauki ba tareda É“ata lokaci ba.

Da farko dai za'a nuƙo garin dabinon ko ayi blending din dabinon da ruwa kaɗan, a zuba a cikin wani madauki mai kyau, sannan a kawo garin gishima kamar misalin cokali goma, garin citta cokali biyar a zuba a ciki, sannan sai a kawo zuma kamar kofi ɗaya da rabi a zuba akai a cakuɗa sosai sannan a riƙa shan wannan haɗi cokali biyu sau uku a rana. Abun nufi shine cokali biyu da safe biyu da rana biyu da daddare.

____________________________________

 Sabon haÉ—in Æ™arin ni'ima cikin sauki ga ma'aurata.

A wannan sabon hadi na ni'ima za'a samu 

1. Jan Apple 

2.Madara ta gari sachet biyu 2

 3. Zuma me inganci

Yadda za'a yi haÉ—in.

Da farko dai za'a ɓare apple ɗin a yanka shi ƙanana ƙanana, sai kuma a samu mazubi me kyau a juye madarar gaba-ɗaya, a zuba zuma kamar cokali uku.

Ba'a saka ruwa, idan kuma ba'a samu zuma ba sai ayi amfani da sugar me dunƙule ƙwaya uku 3.

Ana sha sau biyu a rana tsawon kwanaki bakwai 7.

Sai a kula sosai wajen bawa maigida ko kuma uwargida haƙƙinta.